logo

HAUSA

Algeria da Niger da Nijeria sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas da zai ratsa hamadar Sahara

2022-07-29 11:10:04 CMG Hausa

Kasashen Algeria da Niger da Nijeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna ta shimfida bututun iskar gas da zai ratsa yankin hamadar Sahara, wanda kuma zai samar da karin gas din ga nahiyar Turai.

An gudanar da bikin rattaba hannun ne jiya Alhamis a birnin Algiers na Algeria, a gaban ministocin makamashi na kasashen 3, wanda kuma kari ne kan tarukan da bangarorin 3 suka yi a baya.

Ministan kula da makamashi da ma’adinai na Algeria Mohamed Arkab, ya shaidawa manema labarai cewa, taron na jiya ya biyo bayan irinsa biyu da aka yi a Niamey cikin watan Fabreru, da kuma wanda aka yi a Abuja a watan Yuni.

Ya kara da cewa, sun dauki jerin matakai kuma suna samun gagarumin ci gaba wajen aiwatar da aikin mai muhimmanci.

Aikin shimfida bututun gas da ya ratsa hamadar Sahara, katafaren aiki ne da ya hada Algeria da Niger da Nigeria, wanda ake sa ran tsawonsa zai kai kilomita 4,000, kuma zai iya tura iskar gas mai yawan cubic mita biliyan 30 a kowacce shekara. (Fa’iza Mustapha)