logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 30 a wajen birnin Abuja

2022-07-29 13:52:57 CMG Hausa

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Bernard Onyeuko, ya ce a kalla 'yan bindiga 30 ne dakarun tsaron fadar shugaban kasa suka hallaka, yayin da suke farautar 'yan ta’addan da suka yi musu kwantan bauna a karshen mako.

Onyeuko, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Alhamis, ya ce dakarun tsaron fadar shugaban kasar sun hallaka maharan ne yayin da suka bi sawun su, zuwa wasu yankunan Bwari dake wajen kwaryar birnin na Abuja.

Da yake karin haske game da aukuwar lamarin ta wayar tarho, ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Talata, kakakin rundunar Godfrey Abakpa, ya ce tun da fari, dakarun tsaron fadar shugaban kasar sun fuskanci kwantan bauna ne daga mayakan a daren ranar Lahadi, lokacin da suke aikin sintiri, lamarin da ya haifar da jikkatar wasu daga sojojin.    (Saminu Alhassan)