logo

HAUSA

MDD ta yi tir da rikicin Sudan ta Kudu

2022-07-28 12:30:39 CMG Hausa

MDD ta yi tir da rikici tsakanin ’yan tawaye da dakarun sojin gwamnatin Sudan ta Kudu, a jihar Unity mai arzikin man fetur.

Wakilin musamman na Sakatare-Janar na MDD a Sudan ta Kudu, Nicholas Haysom ya yi ga shugaban masu adawar, Stephen Buay Rolnyang da shugaban dakarun gwamnati, su tsagaita bude wuta nan take.

A cewarsa, “rikicin yanki ya riga ya yi mummunan tasiri a kan al’umma. Don haka, muna kira ga dukkan kungiyoyin dake dauke da makamai, su ajiye makamansu su shiga cikin kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya. Wannan ita ce kadai hanyar magance rikice-rikice da kisan ramuwar gayya, tare da wanzar da zaman lafiya mai karko da dorewa.”

Nicholas Haysom ya jaddada cewa, MDD na ci gaba da bibbiyar yanayin na gundumar Mayom, kuma tana goyon bayan shirin zaman lafiya.

Wannan na zuwa ne bayan rikicin na makon da ya gabata, ya yi sanadin mutuwar a kalla sojoji 12, cikinsu har da James Chuol Gatluak, kwamshinan gundumar Mayom, tare da jikkatar wasu 13 a gundumar dake jihar Unity. (Fa’iza Mustapha)