logo

HAUSA

NSCDC ta yi gargadi game da yiwuwar kaddamar da wasu hare-hare a sassan Najeriya

2022-07-28 12:32:22 CMG Hausa

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ko NSCDC a takaice, ta yi gargadin yiwuwar kaddamar da hare-hare a wasu sassan Najeriya, ciki har da babban birnin tarayyar kasar Abuja.

NSCDC ta bayyana hakan ne cikin wata takardar bayani da ta fitar a ranar Litinin, tana mai kira da a jibge dakarun tsaro a wuraren taruwar jama’a, da suka hada da makarantu, da wuraren ibada, da sauran kadarorin gwamnati.

Takardar sanarwar da hukumar ta fitar, mai dauke da sa hannun mataimakin babban kwamandanta mai lura da gudanar da ayyuka Dauda Mungadi, ta bayyana biranen Abuja da Lagos, da jihohin Kaduna, da Kogi, da Zamfara, da Katsina, a matsayin wuraren da gungun ’yan ta’adda ke shirin kaiwa hare-hare.

NSCDC ta ce "Mun samu bayanan sirri dake bayyana shirin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP, na tattara mayaka, da manyan makamai, domin kaddamar da hari a jihar Katsina. Kaza lika wasu bayanan sirrin na cewa, gungun ’yan fashin daji biyu na shirin kaddamar da hare-haren hadin gwiwa, a wasu sassa na arewa maso yamma, da yankin arewa ta tsakiya, da kuma kudu maso yammacin Najeriya."   (Saminu Alhassan)