logo

HAUSA

Jami’an soji 3 sun mutu bayan wani kwanton bauna da aka kai wa jami’an tsaron fadar shugaban Najeriya

2022-07-27 21:06:08 CMG Hausa

  

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami’an soji guda uku sun mutu, bayan wani harin kwanton bauna da wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka yiwa rundunar tsaron fadar shugaban Najeriyar a Abuja, babban birnin kasar a ranar Lahadin da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar dake gadin fadar shugaba kasar, Godfrey Abakpa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho jiya Talata cewa, an yi wa sojojin kwanton bauna ne a hanyar Kubwa zuwa Bwari, yayin d suke kokarin kawar da masu aikata laifukan da suka addabi yankin baki daya.

Larabar nan wasu majiyoyin soji, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan sun bindige jami’ai 2 daga bisani suka arce daga wurin. Kana mutum guda ya mutu a asibitin sojoji a jiyan, yayin da ake yi masa jinyar raunin harbin bindiga da ya samu.(Ibrahim)