logo

HAUSA

Abu Zubaydah da aka yi wa lakabin “dadadden fursuna”

2022-07-27 10:19:10 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, yau “duniya a zanen MINA” na zana wani mutum mai suna Abu Zubaydah, da aka yi wa lakabi “dadadden fursuna” dake tsare a gidan yarin Guantanamo. Hukumar leken asiri ta Amurka ta mai da Abu Zubaydah a matsayin “mutum mafi daraja dangane da batun ta’addanci”, amma ana tsare da shi ba tare da kai masa kara ko yanke masa hukunci ba, inda ake azabtar da shi har tsawon shekaru 20, duk da cewa an taba gabatar da shaidu cewa, shi ba mambar kungiyar Al-Qaeda ba ne.

Bisa kididdigar da asusun Open Society Foundations na Amurka ya bayar, hukumar leken asiri ta Amurka ta kafa irin gidajen kurkuku wadanda su kan keta hakkin Bil Adama a kimanin kasashe da yankuna 54 na fadin duniya, a yayin da mutanen da aka ci zarafinsu sun kai a kalla 136. Amurka mai matukar nanata muhimmancin kare hakkin Bil Adama, ita ma tana yiwa kanta lakabin “Mai kare hakkin Bil Adama”, amma ta yi biris da hakkin Bil Adama na mutane irinsu Abu Zubaydah, to ko hakkin Bil Adama a ganin wasu ‘yan siyasar Amurka na da fuska biyu? (Mai zane: MINA)