logo

HAUSA

An hallaka soja daya da fararen hula hudu a yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru

2022-07-27 11:11:47 CMG Hausa

Majiyar jami’an tsaron kasar Kamaru, ta ce dakarun ’yan aware na kudu maso yammacin kasar sun hallaka wani kwamandan sojoji 1, da wasu fararen hula 4 a yankin Ikiliwindi, yayin wani kwantan bauna da suka yiwa sojoji da safiyar Talata.

Sojin da ya rasa ransa, yana jagorantar wata tawaga ce ta rundunar BIR mai kai daukin tsaro na gaggawa, sun kuma yi arangama da ’yan bindigar ne yayin da suke sunturi a yankin dake da rinjayen masu magana da Turancin Ingilishi.

Majiyar ta ce "Kwamandan ya rasa ransa ne yayin musayar wuta, kuma ’yan bindigar sun tsere bayan dauki ba dadin, amma jami’an tsaro na ci gaba da farautar su".

Yankuna biyu na kasar Kamaru masu amfani da turancin Ingilishi, wato arewa maso yamma da kudu maso yamma, na shan fama da tashe-tashen hankula tun daga shekarar 2017. ’Yan awaren yankunan dai na fatan kafa kasar "Ambazonia" mai cin gashin kanta a yankunan biyu. (Saminu Alhassan)