logo

HAUSA

Kasar da ke haifar da tashin hankali a duniya

2022-07-27 22:06:06 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Wani nazarin da cibiyar nazari ta Cato ta ruwaito a watan Afrilun bana ya yi nuni da cewa, cikin shekaru biyun da suka gabata, a kalla jami’an soja da suka samu horo daga Amurka sun tsara juyin mulki har sau hudu, daya a shekarar da muke ciki a kasar Burkina Faso, daya a bara a kasar Guinea, sauran biyun kuma a kasar Mali. Baya ga haka, kididdigar da aka fitar ta yi nuni da cewa, daga farkon karni na 20, Amurka ta kuma tsara gomman juye-juyan mulki a kasashen Latin Amurka.

Hakika, yadda Amurka ta sha kitsa juyin mulki ko kuma kaddamar da yaki kan wata kasa kai tsaye ko a fakaice, a yunkurin haifar da rikici a wata kasa da ma cimma burin juyin mulkinta, ba boyayye abu ba ne.

A kwanaki baya, tsohon babban jami’in Amurka kana mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin tsaro, John Bolton ya amince cewa, ya taba “taimakawa wajen tsara juyin mulki a wasu kasashe”, abin da ya girgiza al’ummar kasa da kasa. Hakan ya nuna halin kasar ta Amurka na nuna fin karfi a duniya, wato tana tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe yadda ta ga dama ba tare da yin la’akari da dokokin kasa da kasa ba, kuma ta kan kifar da duk wata gwamnati da ba ta yi mata biyayya, kawai sabo da fi karfi.

Mu kalli yanayin da ake ciki a kasashen Libya da Syria da Iraki da Afghanistan……za mu ga irin barnar da Amurka ta haifar musu domin cimma buri da moriyarta, duk da cewa tana wa kanta kirarin mai kare ‘yanci da dimokuradiyya, amma kowa ya ga abin da ta aika a zahiri. Lallai ta cika mai haifar da tashin hankali a duniya.(Mai Zane:Mustapha Bulama)