logo

HAUSA

Sin Da Indonesiya Za Su Samu Ci Gaba Tare

2022-07-27 15:09:06 CMG Hausa

 

Kafin shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya kawo ziyara kasar Sin, masaniyar cibiyar nazarin manufofin kasar Indonesiya Trissia Wijaya ta taba bayyana cewa, kasashen biyu wato kasar Sin da kasar Indeneniya za su ci gajiya daga ziyararsa, musamman ma ga kasar ta Indenesiya. Yanzu haka sakamakon shawarwarin da shugabannin kasashen biyu wato Xi Jinping da Joko Widodo suka yi a jiya Talata, ya shaida hasashen da ta yi.

Yayin shawarwarin na su, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya dace a ci gaba da yin kokari, domin kara zurfafa hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a samu karin sakamako, hakika kasashen biyu suna da makoma iri daya, kuma tabbas ne za su samu ci gaba tare, har hadin gwiwar dake tsakaninsu zai ci gaba da kasance abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa, da ma daukacin kasashen duniya baki daya. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)