logo

HAUSA

Wata Sabuwa…

2022-07-27 17:20:08 CMG Hausa

A yayin da duniya ke fuskantar manyan sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba cikin karni, gami da kalubalen annobar COVID-19 da har yanzu ke yaduwa a sassan duniya, a hannu guda masana sun yi gargadi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana kukan targade sai ga karaya.”

Kwararru sun sha fadawa shugabannin kasashen duniya a lokuta daban-daban, kafin ma cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu saboda wasu dalilai. Kuma yanzu haka, ana fuskantar wannan matsala a yankin kahon Afirka, da ma wasu sassan duniya.

Saboda girman wannan matsala, ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya yi kira da a gaggauta samar da karin kudade, domin tunkarar matsalolin jin kai dake karuwa a yankin kahon Afrika, yayin da yankin ke tsaka da fama da fari. Inda ya yi gargadin cikin rahotonsa na baya-bayan nan da ya fitar a Nairobin Kenya cewa, za a yi asarar rayuka idan ba a samar da karin kudaden ba.

Bayanai na cewa, mutane a yankin kahon Afrika, wadanda ke fama da fari mafi muni da aka gani cikin shekaru 40 da suka gabata, na fuskantar barazanar yunwa, biyo bayan rashin ruwa a damina 4 a jere, a wasu sassan kasashen Habasha da Kenya da Somalia.

Rahoton ya ce, hasashe na nuna cewa, akwai yiwuwar ba za a samu ruwan sama a lokacin damina na bana tsakanin watan Oktoba da Disamba ba, lamarin da zai haifar da iftila’in da ba a taba gani ba. A don haka, akwai bukatar daukar mataki nan take, domin kare matsalolin da ka iya faruwa a watannin dake tafe.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na cewa, akwai makaurata sama da miliyan 6 da 'yan gudun hijira fiye da miliyan 3 a yankin kahon Afirka. Haka kuma akwai wasu miliyoyin al'umma wadanda suke cikin akuba sakamakon bala'un ambaliyar ruwa ko fari. Wannan ita ce aljannar Waina, sama zafi kasa zafi”. Ga matsalar COVID-19, ga kuma wasu matsaloli dake kara kunno kai.

Abun da ya fi muhimmanci yanzu shi ne, ci gaba da tallafawa irin wadannan mutane da suka shiga irin wadannan matsaloli. Baya ga yadda yaduwar annobar COVID-19 ke haifar da kalubale ga gwamnatocin kasashe daban-daban daga dukkan fannoni, wato daga bangaren lafiyar al'umma, zuwa kawar da talauci da samar da guraban ayyukan yi da isasshen abinci. (Ibrahim Yaya)