Tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a duniya shi ne burin jama’ar Sin da Afirka
2022-07-27 11:22:33 CMG Hausa
Batun zaman lafiya da tsaro, sune ginshikin duk wani irin ci gaban da ake fatan samu, kuma muddin babu wadannan muhimman abubuwa guda biyu, hakaki babu abin da zai samu.
Wannan ya sa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, a cikin wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro na Sin da Afirka karo na biyu da ya gudana da kafar bidiyo,ya jaddada cewa, kasashen Sin da Afirka abokai ne na kwarai, kuma abokan hulda, kana 'yan uwa na kwarai, wadanda ke tsayawa tsayin daka a kowane irin hali suna kuma taimakon juna.
Sanin kowa ne cewa, yanzu haka duniya tana fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba gani ba a cikin karni cikin sauri. Kuma har yanzu annobar COVID-19 tana yaduwa, kana kalubalen tsaro daban-daban na ci gaba da bayyana, inda suke haifar da kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba ga daukacin dan Adam.
Xi wanda ministan tsaro kasar Wei Fenghe ya karanta sakon nasa ya ce, tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a duniya, shi ne burin jama'ar Sin da Afirka na bai daya. Har kullum kasar Sin tana kiyaye tsarin hadin gwiwa da fahimtar juna na zahiri, da son yin hadin gwiwa tare da kawayen Afirka, da dagewa kan hada kai, da hadin gwiwa, da tabbatar da tsaro mai dorewa, da kiyaye MDD a matsayin tushen tsarin kasa da kasa, da kiyaye adalci a duniya, da yayata aiwatar da shirin tsaro na duniya, da gina kyakkyawar makomar al'ummar Sin da Afirka na sabon zamani.
Wakilai daga kasashen Afirka da suka halarci taron, sun bayyana cewa, wasikar da shugaba Xi ya aike, ta nuna yadda ya ke dora muhimmanci kan alakar dake tsakanin sassan biyu. Suna masu cewa, hakika Sin sahihiyar kawa ce kuma ‘yar uwar Afirka. Kasashen Afirka sun kuma yabawa kasar Sin, kan irin goyon baya da taimakon da take baiwa Afirka a fannonin zaman lafiya da tsaro.
Sun kuma bayyana fatan karfafa alaka da bangaren Sin, a fannin tuntuba da inganta hadin gwiwa kan fasahohi da kayayyakin aiki, da zaurfafa atisaye da horon dakarun ruwa da fadada musaya a fannoni daban-daban.
An gudanar da taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na kasar Sin da Afirka karo na biyu, bisa taken "Karfafa hadin gwiwa don samar da tsaro cikin hadin gwiwa". Ya kuma samu halartar ministoci da manyan wakilai daga AU da kasashen Afirka kimanin 30.(Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)