logo

HAUSA

An hallaka jami’in wanzar da zaman lafiya na MDD da ’yan sanda 2 a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo

2022-07-27 11:09:28 CMG Hausa

Yayin da ake kara fuskantar tashe-tashen hankula a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, wani jami’in wanzar da zaman lafiya dan asalin kasar Togo ya rasa ransa, tare da wasu ’yan sanda 2, yayin da wani dan sanda 1 ya jikkata, sakamakon wata zanga-zanga da ta barke a Arewacin Kivu.

Rahotanni sun ce wasu fararen hula da ba a tabbatar da yawansu ba sun rasu, yayin tarzomar ta ranar Talata. An dai gudanar da zanga-zanga ne da nufin nuna adawa da ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ko MONUSCO dake aiki a kasar, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce masu tarzoma sun kwace bindigar wani dan sandan kasar Congo, suka kuma bude wuta kan dakarun MONUSCO.   

Mr. Haq ya hakaito kalaman mukaddashin shugaban MONUSCO Khassim Diagne, na Allah wadai da kisan dakarun tsaron tawagar, tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da ma sauran abokan aikin su.

Diagne ya bayyana rashin amincewa da matakin hallaka dakarun na wanzar da zaman lafiya. Yana mai cewa, hakan ya haifar da matukar koma baya, duba da cewa tawagar MONUSCO na aiki ne tare da mahukuntan kasar domin kare fararen hula, da dakile ayyukan dakaru masu dauke da makamai, da karfafa ikon hukumomin gwamnati na gudanar da ayyuka da ba da hidima.

Mr. Haq ya ce, Diagne ya kuma yi kira ga mahukuntan kasar Congo, da kungiyoyin fararen hula, da na al’umma, da su yi tir da duk wani mataki na tada zaune tsaye.  (Saminu Alhasan)