logo

HAUSA

Africa CDC ta yi kira da a kara sa ido da bibiyar masu cutar kyandar biri

2022-07-26 10:25:37 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da takaita yaduwar cututtuka ta Afrika (Africa CDC), ta shawarci kasashen nahiyar da su inganta sa ido da bibiyar masu cutar kyandar biri domin yaki da ita.

Cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar jiya, ta yi kira ga kasashen Afrika su karfafa ayyukan bincike da nazarin yanayin cutar ta kyandar biri.

Sanarwar na zuwa ne, kwanaki biyu bayan hukumar lafiya ta duniya ta (WHO), ta ayyana cutar a matsayin matsalar lafiya ta gaggawa dake bukatar kasa da kasa su mayar da hankali kanta.

Har ila yau, cibiyar ta yi kira ga kasashen su adana rigakafi da magungunan da kayayyakin da ake bukata na jinyar masu cutar.

Bugu da kari, cibiyar Africa CDC ta bukaci kasashen su samar tare da yayata sakonni na gama gari da ma na musamman ga al’ummomi da rukunoni masu rauni. (Fa’iza Mustapha)