logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a gaggauta samar da kudi domin tunkarar matsalar abinci a kahon Afrika

2022-07-26 10:18:25 CMG Hausa

Ofishin kula da agajin jin kai na MDD (UNOCHA) ya yi kira da a gaggauta samar da kudi domin tunkarar matsalolin jin kai dake karuwa a yankin kahon Afrika, yayin da yake tsaka da fama da fari.

Ofishin ya yi gargadin cikin rahotonsa na baya-bayan nan da ya fitar a Nairobin Kenya jiya Litinin, inda ya ce, za a yi asarar rayuka idan ba a samu karin kudi ba.

Ya kara da cewa, mutane a kahon Afrika, wadanda ke fama da fari mafi muni da aka gani cikin shekaru 40 da suka gabata, na fuskantar barazanar yunwa biyo bayan rashin ruwa a yanayin damina 4 a jere, a wasu sassan kasashen Habasha da Kenya da Somalia.

Cikin rahoton, ofishin ya yi gargadin cewa, hasashe na nuna cewa, akwai yuwuwar ba za a samu ruwan sama a lokacin damina na bana, tsakanin watan Oktoba da Disamba ba, lamarin da zai haifar da iftila’in da ba a taba gani ba. A don haka, ana bukatar daukar mataki nan take, domin kare matsalolin da ka iya faruwa a watannin dake tafe. (Fa’iza Mustapha)