logo

HAUSA

An mika lambar yabon zaman lafiya ta MDD ga sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura wa Kongo(Kinshasa) karo na 25

2022-07-26 10:04:22 CMG Hausa

An mika lambar yabon kiyaye zaman lafiya ta MDD ga dukkanin sojojin kiyaye zaman lafiya su 218, da kasar Sin ta tura wa kasar Kongo(Kinshasa) karo na 25, a sansaninsu dake jihar South Kivu ta kasar a jiya Litinin.

Bisa umurnin tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Kongo ta MDD ko MONUSCO a takaice, an shirya bikin mika lambar yabon ga sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura wa kasar a karo na 25 jiya, inda kwamandan rundunar sojojin Deng Liang ya bayyana cewa, dukkanin sojojin kasar Sin sun darajanta yabon da ake yi musu, kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin ba da gudummowarsu ga wanzar da zaman lafiya da bunkasuwar duk duniya.

Tun bayan da sojojin suka fara aiki a kasar a watan Oktoban shekarar bara, dukkaninsu sun nuna kwazo da himma wajen warware matsaloli iri daban daban da ake fuskanta, haka kuma, likitocin tawagar jami’an kiwon lafiya ta kasar Sin, sun samar da tabbacin aikin likitanci ga jami’an tawagar MONUSCO, wadanda yawansu ya kai sama da 4000. (Jamila)