logo

HAUSA

Mutane 240 sun mutu sakamakon zazzabin Lassa da cutar kwalara a Najeriya

2022-07-26 13:32:07 CMG Hausa

Jaridar “The Punch” ta tarayyar Najeriya, ta labarta jiya cewa, sabbin alkaluman da cibiyar kandagarkin cututtuka masu yaduwa ta kasar ta fitar sun nuna cewa, tun farkon shekarar bana zuwa yanzu, mutane 162 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa, inda ake bincikar mutane 5,756 don tantance matsayin su game da cutar, yayin da kuma cutar kwalara ta hallaka mutane 78, ake kuma binciken yanayin mutane 2,523 domin gano ko sun harbu da cutar. (Jamila)