logo

HAUSA

Tobi Amusan ta Nijeriya ta kafa sabon tarihi a tseren tsallake shingaye na mita 100

2022-07-25 11:26:09 CMG Hausa

Tobi Amusan ’yar Nijeriya ta karya matsayin bajinta na duniya a gasar tseren tsallake shingaye na ajin mata na mita 100, a ranar karshe ta gasar zakarun guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, da aka kammala a jiya Lahadi.

’Yar Nijeriyar ta kammala ne a minti 12:12, inda ta karya matsayin bajintar minti 12.20 na BaAmurkiya Kendra Harrison, a watan Yulin 2016.  (Fa’iza Mustapha)