logo

HAUSA

Tanzania ta kaddamar da noman kadada 11,000 na gonaki ga matasa

2022-07-25 14:12:12 CMG Hausa

Hukumomi a Tanzania sun kaddamar da noman gonakin masu sassa daban daban da girmansu ya kai kadada 11,453 ga matasa, jiya Lahadi a Dodoma dake yankin tsakiyar kasar.

Hussein Bashe, ministan kula da ayyukan gona na kasar ne ya kaddamar da noman gonakin kadada 11,453, a matsayin wani bangare na aiwatar da shirin kasar na shigar da matasa cikin ayyukan gona.

Anthony Mavunde, mataimakin ministan ayyukan gona na kasar, ya shaidawa majalisar dokokin kasar a watan Yuni cewa, gwamnatin Tanzania ta ware fili mai girman kadada 20,000 da za a yi amfani da shi wajen shigar da matasa ayyukan gona.

Shirin wanda shi ne irinsa na farko, na da nufin rage matsalar rashin aiki yi da matasan kasar ta gabashin Afrika ke fuskanta. (Fa’iza Mustapha)