logo

HAUSA

Akwai yuwuwar dakatar da ayyukan agaji a Somalia saboda rashin kudi

2022-07-25 11:24:12 CMG Hausa

Ofishin kula da ayyukan agaji na MDD OCHA ya ce, rashin kudi zai tilastawa hukumomin bayar da agaji dakatar da muhimman shirye-shiryen a Somalia.

A cewar ofishin, idan ba a samu kudi nan take ba, za a dakatar da shirye-shirye kamar na tallafin abinci da sinadaran gina jiki da kiwon lafiya da sauran tallafin rayuwa.

Cikin wani rahoto da ya fitar jiya a birnin Mogadishu, game da sakamakon da rashin kudi zai haifar, ofishin OCHA ya ce karin mutane a kasar za su sha wahala, kuma za a yi asarar nasarorin da aka cimma cikin shekaru 10 da suka gabata.

Ofishin ya kuma yi gargadin cewa, matsalar fari a Somalia ta kara kamari, inda kusan rabin al’ummar kasar, wato mutane miliyan 7.7, ke bukatar agajin jin kai ko na kariya.

Har ila yau, ya ce farin ya yi mummunan tasiri kan mutane a kalla miliyan 7, daga cikinsu kuma, dubu 918 sun bar matsugunansu domin neman ruwa da abinci da abincin dabbobi. (Fa’iza Mustapha)