logo

HAUSA

Tsohon kauyen Liujiayuan ya bude sabon babin shiga harkokin wasanni na zamani

2022-07-25 20:53:12 CMG Hausa

Chen Changlin, manomi mai shekaru 62 a duniya, ya sanya karamar riga ta motsa jiki, yana rike da allon hannu na buga kwallon tebur, ya kuma shirya tsaf don shiga gasar manoma tare da sauran masu sha’awar wasanni dake wannan yanki. A duk yammaci a kan ga magidanta da dama cikin irin wannan yanayi a kauyen Liujiayuan, dake gundumar Qishan ta arewa maso yammacin kasar Sin.  

Mazauna kauyen Liujiayuan, mai tarihin shekaru 3,000 wanda ke karkashin birnin Baoji na lardin Shaanxi, suna atisayen wasan kwallon tebur ko “table tennis” a zauruka rufaffu da filaye.

Duk da cewa ba a Liujiayuan aka haife shi ba, Chen yana aikin noman ganyaye da ‘ya’yan itatuwa a wannan kauye a tsawon shekaru, tuni kuma ya samu damar gudanar da rayuwa mai inganci ba tare da fuskantar kangin talauci ba. Chen, wanda ya fara wasan table tennis shekaru sama da 40 da suka gabata, ya gamu da sauran masu sha’awar wasanni da yawa a wannan kauye.

A cewar sa, "Buri na shi ne tattaro masu sha’awar wasan kwallon tebur dake Qishan, yadda za mu zama kungiya guda, mu rika koyo daga juna ".

Burin Chen ya cika bayan shekaru masu yawa, inda ya kai ga buga gasar kwallon tebur ajin da ba na kwararru ba. Hakar sa ta cimma ruwa, lokacin da aka kafa kungiyar kwallon tebur ta manoman Qishan, ko QFTTA a takaice a ranar 9 ga watan Yulin shekarar 2021.

Bikin kaddamar da wannan kungiya, ya samu halartar shugabannin hukumar wasanni ta Shaanxi, da wakilan hukumar kwallon tebur ta kasar Sin, da jami’an karamar hukuma, da ma tsohon zakaran kwallon tebur na duniya Qi Baoxiang.

Chen wanda yake cike da shauki murya na rawa na cewa, "Lokaci ne da ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwa ta. Kungiyar na kunshe da manoma dake kauyuka daban daban, yanzu mun samu kungiyar kwallon tebur ta mu ta manoma".

Burin Chen bai tsaya a nan ba, domin kuwa bayan shekara guda da kafa kungiyar, an shirya gasar kwallon tebur ta Qishan ajin manoma. Karamar hukumar wurin, da kungiyar QFTTA ne suka shirya gasar, wadda ita ce irin ta ta farko da aka gudanar a lardin Shaanxi. Ta kuma hallara masu fafatawa sama da mutum 100 daga kauyuka 25 na Qishan, da makwaftan gundumomi dake Shaanxi.

Chen ya ce "Jimillar monoma 1,300 sun yi rajistar shiga wannan gasa, kuma ta tattaro sassan al’ummun sama da kauyuka 40 dake Qishan. Na yi farin cikin ganin yadda mutanen dake kewaye da ni ke kara kwarewa yayin gasannin dake gudana. Baya ga kara yawan mambobin kungiyar mu dake shiga wannan wasa, mun kuma karfafa ginshikin wasan, muna yawan shirya gasanni tsakanin ‘yan wasan kauyukan dake kewayen nan".

Yayin gasar yini guda da aka gudanar, Chen wanda ya wakilci kungiyar QTTA, ya zamo na 2.

Kyaftin din kungiyar kauyen Liujiayuan Zhou Wenlin, ya ce tun da farko kauyen Liujiayuan ya raba rukunoni 5 na ‘yan wasa maza da mata, domin shiga gasar ta kwallon tebur a gasar, kuma 4 daga cikin su sun wuce matakin rukuni na gasar.

Zhou Wenlin, wanda kuma shi ne sakataren JKS reshen Liujiayuan ya kara da cewa, "Akwai masu sha’awar kwallon tebur a Liujiayuan. Gasar ta kayatar domin kuwa an fafata, musamman wasan da muka buga a wajen yankin Qishan. Ina ganin sauyin da muka samu a wannan kauye yana da nasaba da kwazon Chen, domin ya karfafa mana gwiwa, inda manoma da yawa suka rika shiga harkokin motsa jiki na yau da kullum. Mazauna wannan yanki sun yi amannar cewa, Chen na da kwazon jagorantar su wajen fita daga kangin talauci, da kuma samun kyautatuwar rayuwa ta hanyar inganta kiwon lafiya".

Zhou ya kara da cewa, “Wannan kauye ya shirya wasanni daban daban domin biyan bukatun manoma ta fuskar motsa jiki na yau da kullum. Baya ga wasan kwallon tebur, da kwallon kwando, an kuma fara gudanar da rawar motsa jiki ta Yangko, da sauran wasanni a kauyen. Mazauna kauyen na buga wasan kwallon tebur, da kwallon kwando da sauran  wasannin motsa jiki tare, wanda hakan ke yaukaka alakar su a matsayin iyali guda kuma makwaftan juna. Kauyen Liujiayuan yana kara zama na zamani, kuma mazaunan sa na samun karin ingancin rayuwa ta hanyar wasanni".

A baya bayan nan, ma’aikatar noma da raya karkara, da hukumar raya wasanni, da hukumar farfado da yankunan karkara na Sin, sun yi hadin gwiwar fitar da ka’idoji na samar da ci gaba mai inganci a fannin wasannin manoma, da inganta karfin jikin su cikin tsarin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14. Karkashin manufar kasar Sin ta gina jagorancin bunkasa wasanni da inganta kiwon lafiyar al’umma, manoma suna da bukatar samun kayayyakin wasanni masu inganci, da suka hada da wuraren motsa jiki, da jagorancin kwararru, musamman a wannan lokaci da wasannin ke kara samun karbuwa cikin shekarun baya bayan nan.

A cewar Chen, "Yankunan karkara na kara bunkasa, kuma manoma suna son samun irin rayuwa mai inganci irin ta birane. A yanzu muna da karin zabi na samun nishadi cikin rayuwar mu ta yau da kullum".

A nasa bangare, babban alkalin wasan kwallon tebur, kuma babban sakataren kungiyar kwallon tebur ta Baoji Tian Junqing, cewa ya yi ta karkashin gasar Qishan, ci gaban wasannin manoma ya kyautata karfin jiki da na tunanin mutane, ya kuma karfafa manufar aiki tare tsakanin al’ummun yankin.

A matsayin sa na babban alkalin wasan kwallon tebur Tian, ya ce yana iya ganin karfin hali, da jajircewar manoman dake shiga a dama da su a wasan kwallon tebur.

Ya ce "Kwazon su, da rashin karaya, da rashin tsoro, da sanayyar su game da gasanni, sun karawa wasanni karsashi a yankin, tare da taimakawa manufar farfado da yankunan karkara".

Koci Tian ya kara da cewa "Gudanar da irin wannan gasa ta manoma, baya ga ingiza ci gaban karkara da ake samu, matakin yana kuma alamta ci gaban rayuwar  manoma a fannonin kiwon lafiyar jiki da tunani. Fatan mu shi ne ganin an kara fadada harkokin wasanni a yankunan karkara a dukkanin sassan kasar Sin".