Aikin koyar da yaran Najeriya fasahar lissafi da carbin kidaya ya karfafa kwarin gwiwar Shiryen Ben wajen samun abin dogaro da kai
2022-07-25 14:46:01 CMG Hausa
Da yammacin wata rana a tsakiyar watan Yuni, Shirley Ben, tsaye kan mumbari a dakin taro na wata makaranta a birnin Fatakwal dake kudancin Nijeriya, ta rika kirawa yaran dake kan mumbarin wasu lambobi.
Yara dake dauke da kayayyakin rubutu suka dan yi lissafi kan iska, nan take kuma suka yi rubutu, suka kuma daga suka nunawa masu kallo, sai kuwa wajen ya kaure da sowa.
Wannan shi ne matakin karshe na gasar kidaya da lissafi ta wasa kwakwalwa da wata makarantar koyar da lissafin wasa kwakwalwa ta shirya. A ranar dalibai 300 ne suka shiga matakin farko na gasar, inda a karshe 15 suka yi nasarar fafatawa a matakin karshe.
“Mun horar da daliban na tsawon wani lokaci, kuma suna amfani da carbin kidaya yanzu haka, wajen nuna basirar da suka samu daga kidaya. Don haka da wannan gasa, iyaye da ma kowa da kowa za su iya ganin yadda yara ke iya lissafi cikin sauri ta hanyar amfani da carbin kidaya.” Cewar Shirley mai shekaru 35 wadda ke shugabantar wannan makaranta ta horar da lissafin wasa kwakwalwa, yayin da take zantawa da manema labarai. A cewarta, makarantar na gabatar da matakai 3 na horo, inda a kowanne mataki ake bukatar lokacin karatu na watanni 4. Kuma an zabo dalibai 300 da suka shigar gasar ne daga cikin dalibai 3,000 dake karatu a makarantar ta Fatakwal a yanzu haka, bayan gwaji da aka yi musu a watan Mayu.
Shekaru 4 da suka gabata, bayan shawarar da abokiyar karatunta ta ba ta a kasar Sin, Shirley Ben ta tafi lardin Shandong na gabashin kasar Sin wajen kara fahimtar sirrin wasa kwakwalwar yara.
Lissafi da carbin kidaya ya samo asali ne daga Zhusuan na kasar Sin, wata dabara ta lissafi ta carbin kidaya. An sanya Zhusuan a cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba na hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD ta UNESCO a shekarar 2013. Shirley ta ce, “Na ga yadda yaran Sinawa ke amfani da carbin kidaya wajen lissafi, yana da ban sha’awa sosai, don haka na yanke shawarar kawo wannan ilimin Nijeriya.”
Bayan samun horo na watanni 6 kan carbin kidayar a shekarar 2018, Shirley ta koma birnin Fatakwal, ta kafa makarantar horo, kuma ta jagoranci wani ayari na yayata lissafin wasa kwakwalwa ta hanyar amfani da carbin kidaya a makarantun birnin. Saboda dabarun wasa kwakwalwa na da inganci wajen bunkasa kwarewar lissafi ga yara, malamai da dalibai har ma da iyaye, sun yi gaggawar amincewa da kwasa-kwasan da su Shirley ke gabatarwa.
A yau, makarantar ta na da cibiyoyi 2 na koyarwa kai tsaye a Fatakwal, da kwararrun malamai 10 da sama da makarantu 40 dake hadin gwiwa da su.
Yayin wata zantawa da manema labarai a wajen gasar, Kike David, wata uwa da yaranta biyu ke makarantar lissafin kuma suka shiga aka fafata da su a gasar, ta ce bayan fara samun horo kan lissafi da carbin kidaya, yaranta sun samu kwarin gwiwa tare da kaunar lissafi.
“Muna son karfafawa gwamnati gwiwar sayen wannan shirinta kuma kai shi makarantunmu na gwamnati,” cewarta.
Roberta Ide, shugabar wata makaranta mai zaman kanta, wadda ta kalli gasar, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, kwazon daliban ya yi matukar burge ta, kuma tana sa ran karin makarantu za su yi kokarin ganin an sanya lissafin carbin kidaya cikin tsarin manhajar karatu na Nijeriya.
Ta kara da cewa, “ a baya, ina tunanin kidaya kawai ake iya yi da carbin, amma abun da na gani a yau, ya fahimtar da ni cewa, carbin kidayar wata dabara ce ta wasa kwakwalwa kuma yana da matukar amfani ga koyarwa musammam ga yara.”
A tattaunawar da ya yi da Xinhua ta kafar bidiyo, Li Mianjun, wanda ya assasa cibiyar ilimi ta China Shenmo Education, wanda kuma ake gani a matsayin shugaba kuma wanda ya fara koyar da lissafin wasa kwakwalwa, ya ce lissafin wasa kwakwalwa, wata dabara ce da ta samo asali daga carbin kidaya. Ya ce dabarar, na karfafawa mai koyo gwiwar hasko carbin da kwallayensa da matakansu a zuciyarsa, tare da kammala lissafi ba tare da carbin a zahiri ba.
Wannan dabarar na da tasiri sosai wajen inganta tunani da hankalin yara, cewar Li. Kuma yanzu, bisa la’akari da karuwar tasirin al’adun Sinawa a duniya, carbin kidaya ya bazu a kasashe da dama.
A cewarsa, tun daga shekarar 2018, cibiyar Shenmo ta bayar da kudin kafa makarantun horar da ilimin lissafin wasa kwakwalwa a sama da kasashe 10, cikinsu har da Nijeriya da Rwanda da Tanzania da Zambia.
A yanzu, Shirley Ben da ta samu kwarin gwiwa daga kasar Sin,na da buri mai girma na fadada harkar horar da lissafin wasa kwakwalwa zuwa wasu biranen Nijeriya a cikin shekaru masu zuwa da kuma neman samar da shaidar kwarewa na lissafin a Nijeriya.(Kande Gao)