logo

HAUSA

Yunwa Ba Dimokuradiya Ba Ce

2022-07-23 21:30:16 CMG Hausa

Sharhi daga Bello Wang

Kamfanin watsa labarai na BBC, ya watsa wani labari a kwanan nan, wanda ke cewa jama’ar kasashen Larabawa, suna yanke kauna ga tsarin dimokuradiya irin na kasashen yamma. A ganinsu, tsarin ya hana gwamnati taka rawa yadda ake bukata, a fannonin tabbatar da tsaro da raya tattalin arizki.

BBC ya watsa labarin ne, bisa rahoton da kungiyar binciken ra’ayin jama’a ta Arab Barometer ta gabatar, wanda Michael Robbins, shehun malami na jami’ar Princeton ta kasar Amurka, ya wallafa. Shi kuma wannan malami ya rubuta dalilin da ya sa Larabawa suke yanke kauna ga tsarin dimokuradiya na kasashen yamma, wanda shi ne “mutane na fama da yunwa, suna bukatar burodi.”

Cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, an yi jerin juyin juya hali na daukar tsarin dimokuradiya a wasu kasashen Larabawa. Zuwa yanzu, ko an samu ci gaban harkoki a wadannan kasashe? Amsa ita ce A’a, ba a samu ba!

Idan mun dauki Tunisia, da Lebanon, da Iraki a matsayin misali, a duk wadannan kasashe, an samu sabuwar gwamnati ta hanyar jefa kuri’a, kuma dukkansu sun dauki tsarin dimokuradiya irin na kasashen yamma. Amma zuwa yanzu, jimillar GDP kan kowane mutum a kasar Tunisia ta yi kasa, idan an kwatanta da na shekarar 2011.

Kana kasar Lebanon ma na fuskantar hadarin rushewar tsarin hada-hadar kudi, yayin da kasar Iraki ke fama da matsalar rashin kwanciyar hankali. Duk wadannan abubuwa sun nuna cewa, tsarin dimokuradiya na kasashen yamma, ba wani abu ne dake iya daidaita dukkan matsalolin da ake fuskanta ba.

Ban da kasashen Larabawa, ko a kasashen yamma, jama’a suna da cikakken imani game da tsarin dimokuradiya irin nasu? Ko alama! Tsohon dan majalisar dattawan Amurka Tom Daschle, ya rubuta wani bayani a kwanan baya, wanda aka wallafa shi a shafin yanar gizo na majalissun kasar Amurka, inda a ciki yake cewa, tsarin dimokiradiya na kasar Amurka “yana daf da halaka kan sa”, sakamakon wasu manyan matsaloli da suka shafi zaman rayuwar jama’a, irinsu bambancin launin fata, da kisan gillar da ake yi da bindiga, da rashin daidaito a fannin samun kudin shiga, da hauhawar farashin kaya, da annobar COVID-19, da dai sauransu.

Hakika duk wata kasa na da irin nata al’adu, da yanayin kasa, wadanda suka sha bamban da juna. Saboda haka, da wuya a ce akwai wani tsarin siyasa mafi kyau, wanda ya dace da kowa. Da ma dai an gabatar da akidar Dimokuradiya, don tabbatar da cewa gwamnati za ta yi kokarin kare hakkin jama’a ne, da biyan bukatunsu. Idan ko burodi ma ba ta iya samar musu, ko rayuwa ta zama mai wuya a gare su, ke nan wannan “tsarin dimokuradiya” ba na gaske ba ne. (Bello Wang)