Ghana ta kaddamar da aikin ginin sabuwar tashar ruwa domin saukaka jigilar hajoji tsakanin ta da kasashe makwafta
2022-07-23 17:39:47 CMG Hausa
A jiya Juma’a ne mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya kaddamar da ginin tashar ruwan shigar da manyan hajoji a yankin Savannah na kasar.
Mahukuntan Ghana, na fatan aikin zai taimaka wajen saukaka safarar hajoji, tsakanin kasar da kasashe makwaftanta da ba su da iyaka da teku.
Da yake tsokaci kan hakan, Mahamudu Bawumia, ya ce wannan muhimmin aiki zai kunshi yankin masana’antu na Debre, wanda zai saukaka shigar da manyan kwantainoni, da manyan hajoji daga tashar teku ta Tema dake Ghana, zuwa kasar Burkina Faso, da sauran kasashe makwafta, da ba su da iyaka da teku ta mashigin tafkin Volta.
Kasancewarta ta yi iyaka da tekun Atlantika, tashoshin ruwan Ghana sun zamo zangon shigar da manyan hajoji, zuwa kasashen yankin Sahel da ba su da iyaka da teku, wadanda suka hada da Burkina Faso, da Mali, da jamhuriyar Nijar. (Saminu Alhassan)