logo

HAUSA

Ya kamata a hukunta Japan saboda amincewarta ga shirin zubar da dagwalon makamashin nukiliya a teku

2022-07-23 16:07:15 CMG Hausa

Jiya Jumma’a ne kwamitin tsara shirin makamashin nukiliya na kasar Japan, ya amince da shirin zubar da dagwalon makamashin nukiliya a cikin teku, na kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo wato TEPCO a takaice, al’amarin da ya zama wani mataki mai hadarin gaske da Japan ta dauka.

A halin yanzu, tashar samar da wutar lantarki bisa karfin nukiliya ta Fukushima Daiichi dake Japan, tana ajiye dagwalon ruwan makamashin nukiliya da yawansa ya zarce ton miliyan 1.25. 

Manazarta sun ce, abu ne mawuyaci a iya tace sinadarai masu guba dake cikin dagwalon makamashin nukiliyar, kana, idan an zubar da shi, zai iya bazuwa zuwa sama da rabin yankin tekun Pasifik a cikin kwanaki 57, kana bayan shekaru 10, zai shafi yankunan tekunan duniya baki daya. 

A sabili da haka, tun bayan da gwamnatin Japan ta yanke shawarar zubar da dagwalon makamashin nukiliya a cikin teku a watan Afrilun bara, kawo yanzu, ta sha suka, da fuskantar rashin yarda daga kasa da kasa da ma al’ummar kasar.

Yadda za’a yi domin daidaita kalubalen dagwalon makamashin nukiliya na tashar Fukushima Daiichi, ba lamari ne da ya shafi bangaren Japan kadai ba. Sai dai kuma Japan ta yanke shawarar ne domin muradunta kadai, wato tattalin lokaci da tsimin kudinta, amma hakan ya jefa dukkanin sassan duniya cikin hadari, al’amarin da ya kasance tsantsar rashin imani.

Bisa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan teku ko LOS a takaice, kasa da kasa na da nauyin kiyaye muhallin yankunan teku. Idan Japan ta dage da yin haka, ya dace kasa da kasa su nemi a hukunta ta, da neman diyya bisa doka da oda. (Murtala Zhang)