logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya wallafa bayani a wasu manyan kafafen yada labaran Nijar

2022-07-23 17:01:34 CMG Hausa

Jiya Jumma’a ne, jakadan kasar Sin dake Jamhuriyar Nijar, Mista Jiang Feng, ya wallafa wani bayani a wasu manyan kafafen yada labaran kasar, ciki har da jaridar Niger Inter. Bayaninsa, mai taken “zumuntar Sin da Afirka ta shiga zukatan al’umma, hadin-gwiwar su kuma babu tsayawa”, ya nuna wasu muhimman nasarorin da aka cimma, a fannin fadada hadin-gwiwar Sin da Afirka.

Bayanin ya ce, mu’amalar da aka yi tsakanin manyan shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka, ta aza tubali mai inganci ga kyautata dankon zumunta tsakanin bangarorin biyu.

An yi taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCOC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka a birnin Dakar na kasar Senegal a shekarar da ta shude, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana wasu muhimman ra’ayoyinsa hudu, game da gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamani, da sanar da wasu muhimman ayyuka tara, a fannin habaka hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, al’amarin da ya kafa sabuwar alkibla ga alakokin bangarorin biyu.

Bayanin jakada Jiang ya kara da cewa, kasar Sin na kara inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a kasashen Afirka, da goyon-bayan ayyukan raya masana’antu, da zamanantar da aikin gona. Kaza lika a halin yanzu, kamfanonin kasar Sin na gudanar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kandadji, da aikin hako ma’adinin man fetur na Agadem a Nijar yadda ya kamata, al’amuran da za su taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasar. (Murtala Zhang)