logo

HAUSA

Shugaban Nijar Bazoum ya gabatar da jawabi a taron ci gaban matasa na duniya

2022-07-22 09:24:33 CMG Hausa

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya aike da sakon bidiyo ga dandalin raya matasa na duniya da aka bude jiya Alhamis a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A cikin jawabin nasa, Shugaba Bazoum ya ce, yana fatan kasashen duniya, za su ba da muhimmanci ga harkar ilimi, da kara zage damtse wajen samar da ayyukan yi ga matasa,da kasuwanci da kirkire-kirkire, da kuma taimakawa matasa zama manyan gobe.

Taron mai taken "Samar da ci gaban matasa, da inganta makoma ta bai daya", ya samu halartar baki sama da 100 daga kasar Sin da kasashen waje, da wakilan matasa kusan 2,000 daga kasashe sama da 100 ta kafar bidiyo da kuma a zahiri.

Manufar wannan dandali ita ce, hada karfi da karfe, don aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030. An raba taron zuwa jigogi guda 4: Na farko shi ne "Aikin yi da harkokin kasuwanci", sai batun "Sauyin yanayi da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba", akwai "Tattalin Arziki na zamani", sai batun "Ilmi da ya kunshi kowa da kowa kuma mai inganci ", wanda zai gabatar da shawarwarin kasa da kasa ga fifikon ci gaban matasa, ga duniya, don kaddamar da ci gaban matasa a duniya, sai kuma shirye-shirye masu alaka da aikin da aka tsara gudanarwa. (Ibrahim)