logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 15 tare da shafar sama da mutane 23,000 a Nijar

2022-07-22 09:38:18 CMG Hausa

 

Ma'aikatar tsaron farin kaya ta Jamhuriyar Nijar, ta sanar a jiya Alhamis cewa, ya zuwa yanzu, ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a daminar bana, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 15 tare da jikkata sama da mutane 23,000 a fadin kasar. Yankunan da lamarin ya fi shafa, su ne Zinder, da Maradi da kuma Diffa.

Rahotanni na cewa, a shekarar da ta gabata, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 70 a fadin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta kuma shafi sama da mutane 200,000.(Ibrahim)