logo

HAUSA

Nijeriya na duba yuwuwar haramta amfani da Babura da hakar ma’adinai domin yaki da ta’addanci

2022-07-22 11:09:47 CMG HAUSA

 

Majalisar tsaro ta Nijeriya, tana duba yuwuwar hana amfani da Babura da ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasar, domin yaki da ayyukan ta’addanci.

Yayin taron majalisar da aka gudanar jiya karkashin shugaban kasar Muhammadu Buhari, jami’ai sun nazarci batun haramta amfani da Babura da hakar ma’adinai, a matsayin wani bangare na dabarun majalisar na yaki da ta’addanci da toshe kafafi da kuma hanyoyin samun kudin gudanar da muggan ayyukan.

Bayan taron, atoney-janar, kana ministan shari’a na kasar Abubakar Malami, ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnati za ta gudanar da bincike domin duba yiwuwar hana amfani da babura da ayyukan hakar ma’adinai, musammam ma amfani da babura, wanda shi ne abun da ’yan ta’adda suka saba da shi. Ya ce za su iya amfani da babura wajen sauya abun da suka samu daga hakar ma’adinai zuwa sayen makamai.

Ya kara da cewa, gwamnati na sane da mummunan tasirin wannan kuduri ga tattalin arziki, amma kuma, ya zama wajibi a tabbatar da tsaron kasar, bisa la’akari da yadda ayyukan ta’addanci suka sauya daga samun kudi daga mutane, zuwa samun kudi daga hakar ma’adinai da neman kudin fansa. (Fa’iza Mustapha)