logo

HAUSA

Dokar da ta tanaji damar samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni ta Amurka za ta haifarwa kasar da cikas

2022-07-22 22:05:27 CMG Hausa

Kwanan nan ne majalisar dattawan Amurka, ta zartas da shirin kada kuri’a dangane da wata dokar da ta tanaji damar samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni, don share fage ga majalisun dattawa da wakilan kasar da su kada kuri’a a kan ta.

Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce, shirin dokar zai samar da kudi fiye da dala biliyan 50, don raya sana’ar da ta shafi kera sassan hada na’urorin laturoni na kasar, wanda zai kawo tsaiko ga kamfanonin da suka samu tallafin kudi a wannan fanni, su zuba jari a kasar Sin.

Alkaluman da aka bayar sun nuna cewa, a shekara ta 2021, yawan kudin cinikin da kamfanonin da suka gudanar da ayyukan samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni na kasar Sin suka yi, ya karu da kaso 18 bisa dari, adadin da ya zarce kudin Sin tiriliyan 1. Sa’annan kididdigar ta nuna cewa, a watanni 12 da suka gabata, a duk watanni uku, daga cikin kamfanonin samar da rukunin ababen hada na’urorin laturoni wadanda suka samu saurin ci gaba a duniya, guda 19 na kasar Sin ne.

A yayin da ake kara samun dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, idan kasar Amurka ta kara raba sana’o’i da gangan, za’a haddasa rudani ga sana’o’in duniya, da tsananta matsalar samar da isassun rukunonin ababen hada na’urorin laturoni. Ya dace ‘yan siyasar Amurka su kara aikata alheri, don tabbatar da gudanar da sana’o’in duniya yadda ya kamata, saboda duk wani yunkuri na maida hannun agogo baya, ba zai ci nasara ba, domin kowa ya shuka zamba, ita zai girba. (Murtala Zhang)