Yadda wasanni ke hade kan kabilu daban daban a Xinjiang
2022-07-21 15:31:09 CRI
Kungiyar kwallon kwando mai lakabin “Commanders”, dake hade kan ‘yan wasa da ba na ajin kwararru ba, sananniyar kungiya ce a birnin Urumqi fadar mulkin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, wadda ke arewa maso yammacin kasar Sin.
Kyaftin din kungiyar mai suna Make, wanda ke sana’ar aski, dan asalin kabilar Hui, ya bayyana tasirin wannan kungiya, yana mai cewa, "Mutane sun san mu ba wai saboda mun kware a wasan kwallon kwando ba, sai dai kawai saboda mun kai sama da shekaru 10 muna wasa tare".
Baoyin, dadadden dan wasan kungiyar ne daga karamar kabilar Mongolia, ya kuma bayyana cewa, kusan akwai ‘yan wasa 50 daga kabilu daban daban har 7 a wannan kungiya, wadanda suka hada da ‘yan kabilar Han, da Uygur, da ‘yan Mongolia da Dongxiang. Suna da sana’oi mabanbanta, kuma wasu sun san juna a wuraren ayyuka da makarantu, amma mafi yawan su a wurin wasan kwallon kwando suka hadu.
‘Yan wasan na amfani da daukacin lokacin hutun su domin buga kwallon kwando tare. Zumunci yana kulluwa tsakanin mutane da ba su san juna ba a harkokin yau da kullum, har ta kai sun zama al’umma dake kaiwa ga ziyartar juna, da hada wasanni da tafiye-tafiye na nishadi tsakanin su.
Kungiyar “Commanders” misali ne na yadda wasanni ke hada zumunci tsakanin mabanbantan kabilu.
Du Baozhu, daya ne daga tsofaffin ‘yan kungiyar kwallon goro ta “hockey” ta kasar Sin, wanda ya koma Tacheng, dake arewa maso yammacin Xinjiang a shekarar 2014, ya kuma kafa wata kungiyar kwallon hockey a wata makarantar firamare. Cikin shekaru 2 kacal, kungiyar sa ta lashe gasanni daban daban da aka shirya a matakin kasa.
Babban kocin kungiyar Li Ming, ya ce "Kungiyar ta kunshi dalibai daga kabilu daban daban, wadanda za su kai 8 zuwa 9, da suka hada da Han, da Daur, da Kazak da sauran su. Ta hanyar wasanni, yaran ‘yan kabilu daban daban, suna koyo tare da girma tare”.
Kamar dai sauran sassan kasar Sin, al’ummun dake zaune a Xinjiang su ma na taka muhimmiyar rawa, wajen shirya harkokin wasanni a matakai na al’umma.
Elyar Amat, dalibin jami’a ne dan kabilar Uygur, wanda ya je Kashgar hutu daga jami’ar Jilin. A wannan lokaci na bazara, Amat zai kasance cikin tawagar da za ta wakilci yankin sa a gasar kwallon kafa da za a buga.
A cewar sa, "Na yi farin ciki da haduwa da al’ummun yanki na. hakan dama ce ta kyautata abota da cudanta tsakanin mu”.
Da yake tsokaci kan harkokin wasanni a wannan jiha ta Xinjiang, Turahun Abdurahman, mataimakin shugaban kulaf din kwallon kafa na jihar Xinjiang, ya ce an shirya gudanar da sama da wasanni 10,000 yayin gasar kwallon kafa mai kunshe da ‘yan wasa biyar-biyar a Kashgar, wasannin da ake fatan za su raya harkar kwallon kafa tsakanin al’ummu, da ingiza cudanya tsakanin daukacin jama’ar kabilun jihar daban daban.
Liuxing street, unguwa ce mai kunshe da al’ummu daga kabilu daban daban, wadda take a yankin Yining, ta kuma zamo wuri mai ban sha’awa da mutane ke son ziyarta, saboda al’adu daban daban masu kayatarwa, da wasanni da ake nunawa a cikin ta.
Cui Xiaojuan, ‘yar yawon shakatawa ce daga lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, wadda ta ce ta fi sha’awar wasannin raye-raye na dandali da ake yi a titin Liuxing, sama da sha’awar ta ga gine-gine da nau’oin abinci.
Cui ta kara da cewa, "Mazauna wannan wuri sun shaida min cewa, wadannan masu raye raye ‘yan kabilu daban daban ne, suna kuma sha’awar koyon rawa daga junan su, wanda hakan ya yi matukar burge ni".