logo

HAUSA

Hauhawar farashin kayayyaki a Afrika ta kudu ya kai kashi 7.4%

2022-07-21 10:53:38 CMG HAUSA

 

Hukumar kididdigar kasar Afrika ta kudu, ta sanar a jiya cewa, hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu daga kashi 6.5% a watan Mayu zuwa kashi 7.4% a watan Yuni na bana, adadin da ba a taba garin irinsa ba tun a watan Mayu na shekarar 2009.

Farashin man fetur a watan Yuni, ya karu da kashi 45.3% bisa na makamancin lokaci na bara, karuwa mafi girma da ba a taba gani ba a tarihi.

Haka kuma, farashin burodi da hatsi, sun karu da kashi 11.2% kan makamancin lokaci na bara, yayin da farashin garin masara ya karu da kashi 5.2% a cikin wata guda, kana a karshen watan Yuni, farashin nama ya karu da kashi 19% bisa makamancin lokaci na bara.

A halin yanzu, hauhauwar farashin kayayyaki a Afirka ta kudu, ya zarce hasashen da babban bankin kasar (SARB) ya yi, wanda ya kai kashi 4% zuwa 6%, wanda hakan na iya jan hankalin kwamitin kula da manufofin kudi na kasar, don kara yawan kudin ruwa a yau. (Amina Xu)