logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat: Huldar Afrika da Sin abin koyi ne

2022-07-21 10:36:54 CMG HAUSA

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana a jiya Laraba cewa, huldar dake tsakanin AU da kasashen Afrika da Sin abin koyi ne a wannan zamani.

A kuma jiya, Moussa Faki Mahamat ya karbi takardar aiki na sabon shugaban tawagar Sin a kungiyar, kana jakada na musamman, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, Hu Changchun. Moussa Faki ya darajanta dadadden zumuncin dake tsakanin Afrika da Sin, da kuma ci gaban da bangarorin biyu suka samu a hadin kansu, yana mai jaddada cewa, huldar dake tsakanin AU da kasashen Afrika da Sin, abin koyi ne a wannan zamani. Ya ce, AU na fatan kara hada kai da Sin, don gaggauta tabbatar da taron Dakar na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da sakamakon hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a kara amfanawa al’ummomin bangarorin biyu.

A nasa bangare, Hu Changchun ya nuna cewa, AU tana taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar dunkulewar nahiyar Afrika waje guda, da daidaita hadin kan kasashen Afrika wajen tinkarar COVID-19, da kuma shiga tsakanin a kan batutuwan dake jawo hankalin bangarori daban-daban a yankin. Ya ce, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakarta da AU, tana mai fatan zurfafa hadin kai da kasashen Afrika bisa manyan tsare-tsare da amincewa da juna, ta yadda za a ingiza huldar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)