logo

HAUSA

Amurka ba za ta iya bata sunan Xinjiang ba

2022-07-21 09:42:39 CMG Hausa

A kwanakin nan ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gabatar da abin da ake kira wai "kudirin dokar dakile kisan kiyashi da ta’adanci" ta shekarar 2022, rahoton da ta saba fitarwa a kowace shekara ga majalisa, ta kuma ba da "Dabaru na hasashe, neman hanawa, da yin raddi ga ayyukan ta'addanci" a tarihin Amurka. inda aka sake sanya batun "kisan kare dangi" da batun "sanya aikin tilas" da sauran batutuwa da suka shafi yankin Xinjiang na kasar Sin a cikin rahoton.

Rahoton na shekara-shekara na shekarar 2022, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta gabatar, ya ci gaba da bin diddigin dabarun yada jita-jita, da neman bata sunan al'ummar jihar Xinjiang, tare da neman mayar da martani ga abin da ake kira wai "Dokar kare tilasta aikin kwadago ta Uygur" wadda ta fara aiki a ranar 21 ga watan Yunin wannan shekara. Dukkansu sun yi amfani da batun kare hakkin dan-Adam, a matsayin wani makami na mayar da Xinjiang saniyar ware, a tsarin ayyukan masana’antun saka kaya na duniya, da haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar Xinjiang, ta yadda za a cimma burin dakile ci gaban kasar Sin.

A zahiri, duk wani rahoto, ko dabaru ko lissafin da Amurka za ta fitar, ba za ta iya bata sunan jihar Xinjiang ta kasar Sin ba. Domin abin da al'ummar duniya ke gani shi ne, jihar Xinjiang dake samun bunkasuwa cikin aminci, da wadata ba kuma tare da wata rufa-rufa ba. Don haka, wannan ba shi da nasaba da abin da ake kira wai "kisan kare dangi" da "aikin tilas". (Ibrahim)