logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya jinjinawa kasar Sin bisa kammala sabon ginin majalisar dokokin kasar

2022-07-21 09:54:57 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, jiya Laraba ya kewaya sabon ginin majalisar dokokin kasar dake tsaunin Hampden, mai tazarar kilomita 18 daga arewa maso yammacin Harare, babban birnin kasar da aka kammala.

Kasar Sin ce dai ta samar da kudade tare da gudanar da aikin sabon ginin majalisar a matsayin kyauta ga kasar dake kudancin Afirka.

Shugaba Mnangagwa ya ce, babban ginin dake kan tsaunin Hampden mai tarihi, gado ne ga al'ummar Zimbabwe dake tafe.

Mnangagwa wanda mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga ya rufa masa baya, ya yi mamakin katafaren ginin mai hawa shida, mai kunshi da kyawawan gine-gine, masu shigar kasashen biyu, wato Zimbabwe da Sin.

Mnangagwa ya yi amfani da wannan dama, wajen jinjinawa gwamnatin kasar Sin, bisa cika alkawarin da ta yi, na gina sabon ginin majalisar dokokin kasar, da sauran ayyukan more rayuwa daban-daban, wadanda suke mataki daban-daban na kammalawa.

Ya kuma gode wa dan kwangilar rukunin kamfanin gine-gine na Shanghai na kasar Sin, saboda aiki mai kyau da aka yi, duk da tsaikon da aka samu sakamakon annobar COVID-19. (Ibrahim)