logo

HAUSA

Najeriya: Kamfanin NNPC ya zama kamfanin kasuwanci mai zaman kan sa

2022-07-20 21:14:38 CMG Hausa

A jiya Talata ne aka kaddamar da kamfanin mai na kasuwanci mai zaman kan sa na Najeriya, wanda aka yiwa lakabi da NNPC Limited, bayan da aka gudanar da gyare-gyare ga sashen albarkatun mai na kasar, biyo bayan dokar PIA da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a bara.

Kafin sauyin, kamfanin mai na NNPC, ya shafe shekaru 45 yana aiki karkashin mallakar gwamnatin Najeriya.

A yayin kaddamar da kamfanin a jiya Talata, shugaba Buhari ya ce,  Nijeriya na gudanar da gyare-gyare ga sashen albarkatun mai ne don fatan ganin karfafa ikonsu na taka rawar gani a hada hadar kasuwannin makamashi ta kasa da kasa, a halin da ake ciki da kuma nan gaba.   (Saminu Alhassan)