logo

HAUSA

Aljeriya na son karfafa hadin gwiwa da Sin

2022-07-20 11:13:26 CMG Hausa

Shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya ce kasarsa na son karfafa mu’ammala da hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban.

Shugaban ya fadi zancen ne a jiya Talata, yayin da yake karbar takardar shaidar mukamin jakada da sabon jakadan kasar Sin a Aljeriya, Li Jian, ya mika masa. Shugaban na Aljeriya ya kara da cewa, kasarsa na daukar huldarta da kasar Sin da matukar muhimmanci, kana ta na son yin kokari tare da bangaren Sin, don raya huldar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, jakada Li na kasar Sin, ya taya kasar Aljeriya murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai, da yadda aka gudanar da babbar gasar wasannin motsa jiki ta bahar Rum a birnin Oran na kasar. A cewar jami’in na kasar Sin, tun bayan da bangaron Sin da Aljeriya suka kulla huldar diplomasiya, sun yi ta kokarin rufa wa juna baya, tare da nuna sahihanci. Ya ce yadda suke dukufa wajen kyautata huldar dake tsakaninsu, zai iya zama misali ga sauran kasashe, kana hadin gwiwarsu ya haifar da dimbin sakamako. Ya kara da cewa, kasar Sin na son ci gaba da karfafa zumuntar da ke akwai tsakaninta da Aljeriya, da kara sabbin abubuwa cikin huldar abota da aka kulla tsakanin bangarorinsu, wadda ta shafi manyan tsare-tsare a fannoni daban daban. (Bello Wang)