logo

HAUSA

Yankin Xinjiang, wuri mai ni’ima ne da al’ummun Sinawa ke jin dadin zama da yin aiki

2022-07-20 09:16:15 CMG Hausa

A ci gaba da rangadin sassan kasar Sin da yake yi daga lokaci zuwa lokaci, a wannan karo babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya ziyarci jihar Xinjiang, inda ya ziyarci jami'ar Xinjiang, da yankin tashar kan tudu ta kasa da kasa ta Urumqi, da al'ummar Guyuanxiang dake gundumar Tianshan, da gidan adana kayan tarihi na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta dake birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang, da birnin Shihezi, da wani birni daban na Turpan na jihar.

Yayin wannan ziyara, ya fahimci yadda ake aikin zakulo masu hazaka, da yadda ake daidaita matakan yaki da annobar COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa tare, da inganta hadin kan kabilu da bunkasuwa, da karfafa fahimtar al'ummar kasar Sin, da dai sauransu.

Haka kuma, shugaba Xi ya kalli wani wasan gargajiya na kabilar Kirgiz mai suna Manas, da aka shirya a gidan adana kayan tarihi na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. Inda ya bayyana cewa, kiyaye al'adu irin na Manas, wata al’ada ce ta 'yan tsirarun kabilu da kuma al'ummar kasar Sin. Yana mai jaddada kara kokarin kiyayewa da yayata al’adu.

Sauran wuraren da ya ziyarta yayin wannan rangadi, sun hada da mazauna garin Guyuanxiang, inda ya ce, dole ne a kara kaimi, ta hanyar dogaro da al’umma. Don haka, ya bukaci hukumomi su kara himma, wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma, don kara koyo da biyan bukatun jama’a da amfanar da mazaunan dukkan kabilu.

Xi ya ziyarci yankin tashar kan tudu ta kasa da kasa ta Urumqi yana mai cewa, yayin da ake samun ci gaba a hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, a hannu guda kuma, ba za a bar jihar Xinjiang a baya ba, sai ma ya zama yanki mai muhimmanci, kuma wata cibiya. Ya kuma yi na’am da ci gaban da ma'aikatan suka samu, yana mai karfafa musu gwiwar kara kokarin yin aiki don samun gagarumar nasara, ya kuma ziyarci birnin Shihezi da Turpan, da gidan adana kayan tarihi na ma’aikatan dake aikin samar da kayayyaki da kare kan iyakar Xinjiang (XPCC) da kuma wani bangare da ke karkashin sashen XPCC. Wannan na kara nuna yadda mahukunta kasar Sin ke mayar da jama’a a gaban komai, karayata bayanan karya da kasashen yamma ke watsawa game da yankin, don neman bata sunan kasar Sin da ma hana ci gabanta. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)