logo

HAUSA

An shirya taron farko na karamin kwamitin aikin gona na kwamitin gwamnatocin kasashen Sin da Najeriya

2022-07-20 20:01:44 CMG Hausa

Kwanan baya, aka gudanar da taro na farko na karamin kwamitin aikin gona, na kwamitin gwamnatocin kasashen Sin da Najeriya ta kafar bidiyo.

A yayin taron, bangarorin biyu sun waiwayi nasarorin da aka cimma, a hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, a fannonin amfani da fasahohin aikin gona, da cinikayyar noma, da ingancin abinci, da horar da kwararru, da kuma manyan ababen more rayuwa da dai sauransu, tare da yin mu'amala sosai kan kara sa kaimi, ga ciyar da hadin kai mai inganci a kasashen Sin da Najeriya gaba.

Kana bangarorin biyu sun bayyana aniyarsu, ta kara zurfafa hadin gwiwa, da zurfafa alaka, da ayyukan da suka shafi "Ayyuka tara", na taron ministoci karo na takwas, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wadanda aikin hadin kan laimar kwado ya wakilta, ta yadda za a ci gaba da kyautata jin dadin jama'ar kasashen biyu, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

Mataimakin ministan noma da yankunan karkara na kasar Sin Ma Youxiang, da babban sakatare a ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar Najeriya Ernest Afolabi Umakhihe ne suka jagoranci taron. Shi ma Ambasada Cui Jianchun daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya ya halarci taron ta yanar gizo. (Mai fassara: Bilkisu Xin)