logo

HAUSA

MDD ta ware dala milyan 15 domin tunkarar yunwa a CAR

2022-07-20 10:45:23 CMG HAUSA

 

Shugaban ayyukan tallafin gaggawa na MDD Martin Griffin, ya amince da fitar da dala miliyan 15 domin samar da tallafin abinci ga mutane 200,000 dake fama da rashin abinci a jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya ruwaito cewa, Martin Griffin, wanda kuma mataimakin Sakatare Janar na majalisar ne, ya fitar da kudin ne daga asusun tallafin gaggawa na MDD.

A cewar Farhan Haq, za a yi amfani da kudin ne wajen samar da tallafin abinci da sinadaran gina jiki da kiwon lafiya da ruwan sha da tsaftar muhalli da ta jiki da matakan kariya daga cututtuka. Yana mai cewa, kimanin mutane miliyan 2.2 ko kaso 36 cikin dari na al’ummar kasar ba su da isasshen abinci.

Ya kara da cewa, galibin mutanen na rayuwa ne a yankunan dake fama da rikice-rikice, inda rashin tsaro da matsuguni, suka rage yawan gonaki da damar isa kasuwanni.

Ya kuma yi hasashen cewa, matsalar yanayi da rikice-rikice, za su kara ta’azzara lamarin, inda farashin kayayyaki zai karu zuwa kaso 70 a watan Augusta. (Fa’iza Mustapha)