Kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen gina babban ginin majalisar dokokin Zimbabwe
2022-07-19 14:41:56 CMG Hausa
Aikin gina babban ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe, aiki ne mafi girma da kasar Sin ta samar da tallafin gudanar da shi a kudancin nahiyar Afirka. Wani kamfanin gine-gine na kasar Sin, da ake kira Shanghai Construction Group (SCG) ne ya dauki nauyin gina shi.
Tun daga watan Satumbar shekara ta 2018, har zuwa yanzu da aka kammala ginin, Cai Libo ya jagoranci ma’aikatansa, wadanda suka shawo kan kalubaloli da matsaloli da dama, har suka kai ga cimma nasarar gina irin wannan gini, wanda ya zama tamkar babbar alama a Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe. Cai ya ce, “Ta hanyar gudanar da aikin gine-gine a kasashen ketare, yana fatan tallata fasahohin kasar Sin zuwa ga duk duniya”.
An nada Cai Libo, a matsayin shugaban aikin gina babban ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe a watan Satumbar shekara ta 2018. A karkashin jagorancinsa, an kaddamar da aikin ba tare da bata lokaci ba. Cai ya ce:
“A wancan lokaci, ina aiki a hedikwatar kamfaninmu dake kasar Sin. Saboda yardar da shugaban kamfanin ya yi da ni, da ayyukan da na taba gudanarwa a kasashen waje, an ba ni irin wannan babban aiki. Bisa la’akari da moriyar kamfaninmu, da muhimmancin aikin, ina alfahari sosai da samun wannan dama, shi ya sa na karbi aikin. A ranar 25 ga watan Satumbar shekara ta 2018, na tafi Zimbabwe don fara aikin.”
An dai gudanar da aikin gina babban ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe ne a wani tsauni mai suna Hampden, mai tazarar kilomita 20 daga arewa maso yammacin birnin Harare, wanda ke da fadin murabba’in mita dubu 33. Da fari an yi shirin kammala aikin a watan Maris din shekara ta 2021, amma annobar COVID-19 da ta bulla ba zato ba tsammani, ta haifar da cikas da kalubaloli daban-daban. Mista Cai Libo ya ce:
“Mun gamu da matsaloli da dama a yayin aikin gine-gine, musamman saboda annobar COVID-19 da ta bulla a shekara ta 2020. Tun bullar cutar a kasar Sin a farkon shekara ta 2020, mun fuskanci matsalar tura ma’aikatan gine-gine daga kasar Sin zuwa Zimbabwe, har ma farashin kayan gine-gine, da na jigilar manyan sundukai, da na tikitin jirgin sama duk sun yi tashin gwauron zabi.”
Cai da abokan aikinsa, sun nuna jajircewa wajen haye wahalhalu, da biyan bukatun aikin gine-gine, a yayin da suke daukar kwararan matakan kandagarkin yaduwar cutar. Kwalliya ta biya kudin sabulu, har sun kawo karshen gaba dayan aikin ginin babban ginin majalisar dokokin Zimbabwe, a watan Mayun shekarar da muke ciki. Kuma nan bada jimawa ba, za’a mika shi ga bangaren Zimbabwe don soma aiki.
Babban ginin majalisar dokokin Zimbabwe da kamfanin kasar Sin ya samar da taimakon ginawa, gini ne na zamani, wanda zai kyautata muhallin gudanar da taro, da aiki na ‘yan majalisar dokokin kasar, wanda zai zama tamkar alama ce a wurin. Mista Cai Libo ya ce, wannan aiki zai taimaka sosai ga bunkasa sabon garin:
“Wurin da muka gina babban ginin majalsiar dokoki, wuri ne da gwamnatin kasar Zimbabwe ta tsara don gina sabon garin Harare. Ginin zai kyautata hanyoyin sufuri, da na’urorin samar da ruwa, da wutar lantarki dake kewayen sa, da samar da kyakkyawan sharadi ga aikin raya sabon garin. Har wa yau, wannan gagarumin aiki ya dace da manufar diflomasiyyar kasar Sin, wato hada mafarkin kasar Sin da na duniya gaba daya, da kara hada kai don samun moriya tare, da ci gaba da daga matsayin hadin-gwiwa tare da kasashe masu tasowa, da zama wani muhimmin al’amari cikin muradun kasar Zimbabwe nan da shekara ta 2030.”
Cai ya kara da cewa, gaba daya, an yi hayar ma’aikatan wurin sama da 800 don aikin gine-gine, kuma ma’aikatan kasar Sin sun jajirce wajen koya musu fasahohin zamani, ta yadda suka samu karin damammakin aiki da rayuwa.
Wani ma’aikacin gine-gine na kasar Zimbabwe mai suna Gilbert Maorede ya ce, halartar aikin gine-gine na babban ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe, ya sa ya kara samun kwarewa a fannnin aikin gine-gine, inda ya ce:
“Mutanen kasar Sin suna da fasahohin ci gaba, mun koyi abubuwa da yawa daga wurinsu. Bayan da muka gama wannan aiki, za mu iya ci gaba da aikin gine-gine bisa fasahohin zamanin da muka koya, da ci gaba da halartar irin wannan gagarumin aiki. Gaskiya mun karu sosai.”
Yayin aikin gine-gine na tsawon shekaru sama da 3, bangaren kasar Zimbabwe yana maida hankali sosai a kansa. Ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya ziyarci wurin aikin, inda ya jinjinawa kokarin ma’aikatan wurin, da godewa kasar Sin saboda tallafin da ma’aikatanta suka bayar. Mnangagwa ya jaddada cewa, saboda shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta bullo da ita, an samu damar fara raya muhimman ababen more rayuwar al’umma da yawa, har ma Zimbabwe ta kara cudanya, da mu’amala da sauran kasashen duniya.
Shugaba Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa:
“Muna matukar godiya ga gwamnatin kasar Sin, saboda goyon-bayanta na dogon lokaci ga babban aikinmu na samar da ci gaban kasa. Mun yaba da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, saboda a karkashinta, an fara gina wasu muhimman ababen more rayuwar al’umma a Zimbabwe, ciki har da babban ginin majalisar dokokin kasa. A al’adance, muna ganin Zimbabwe kasa ce da ba ta da iyaka da teku, don haka ba ta iya mu’amala da sauran kasashe. Amma shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ta fadakar da mu cewa, bai dace mu rufe kofar kasarmu ga sauran kasashe ba, ya dace mu kara yin mu’amala da su.”
2022, shekara ce ta 10, da Cai Libo yake aiki a kasashen waje, inda a baya ya taba gudanar da ayyukan gine-gine a kasashen Qatar, da Malawi, da Eritrea da Comoros da sauransu. Ya ce, duk wadannan ayyukan da ya taba yi, suna da babbar ma’ana, kana abun alfahari ne gare shi, inda ya ce:
“Buri na shi ne, gudanar da kowane aikin gine-gine yadda ya kamata, a wani kokari na bayar da gudummawa ga ayyukan tallafawa kasashen waje, da sha’anin hadin-gwiwar Sin da Afirka, da kuma ayyukan da suka shafi shawarar ‘ziri daya da hanya daya’. Sa’annan, a horas da ma’aikatan wurin, don aza tubali mai inganci ga ayyukan hadin-gwiwar Sin da Afirka na nan gaba. Ta hanyar gudanar da ayyukan gine-gine a kasashen waje, ina kokarin bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu, da tallata kyawawan dabaru, gami da fasahohin kasar ga karin kasashe.”
Cai Libo ya ce, halartar aikin gina babban ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe, wani muhimmin aiki ne da ya yi a tarihin sana’arsa, wanda kuma zai ci gaba da bayar da gudummawa a fannin gudanar da ayyukan gine-gine a kasashen ketare, musamman ayyukan da suka shafi shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Murtala Zhang)