logo

HAUSA

Kwarin tubalin tattalin arzikin Sin ya na karawa kamfanonin waje kwarin gwiwar zuba jari

2022-07-19 19:16:36 CMG Hausa

Wani rahoton kafar yada labarai ta china Daily ta kasar Sin, ya ruwaito a yau Talata cewa, kamfanonin kasashen waje na kara imani da tattalin arzikin kasar Sin kuma sun karfafa kudurinsu na fadada zuba jari a kasar Sin.

Wannan baya rasa nasaba da ci gaban tattalin arziki da kasar ta samu cikin rabin farko na bana, inda ya karu da kaso 2.5. Wannan kuma na da alaka da tubali mai kwari da aka gina tattalin arzikin kasar a kai. Yayin da ake fama bullar annobar COVID-19 da wasu matsalolin duniya, hakika kasar Sin ta yi namijin kokari wajen tabbatar da tattalin arzkinta ya bunkasa ta hanyar dabarunta na hangen nesa da kuma bude kofarta ga waje.

Ko a baya-bayan nan, babban bankin kasar ya sanar da kudurinsa na daukar wasu manufofin kudi domin taimakawa dukkan bangarorin tattalin arziki. Har kullum, kasar Sin bata kasa a gwiwa wajen samar da yanayi mai kyau na habakar tattalin arziki, ta hanyar taimakawa dukkan bangarori. Duk da irin bata mata suna da ake yi, karin kamfanonin waje na kara karfafa imaninsu da ita, saboda sun amince da manufofinta, haka kuma ta na kokarin samar musu da yanayi mai kyau da kara habaka bangarorin zuba jari.

Yadda kasar Sin ke jagorantar bangaren fasahohin zamani, ya kara jan hankalin ‘yan kasuwar kasashen ketare. A kullum duniya na sauyawa, don haka, tafiya da zamani ya zama dole muddun ana son samun ci gaba. Kuma kasar Sin ta samar da wannan yanayi inda take karfafa gwiwar kirkire kirkiren sabbin fasahohin zamani, bangaren da ya karawa tattalin arzikin kasar da ma ‘yan kasuwa kuzarin zuba jari.

Haka zalika, yayin da a ko ina a duniya ake fama da hauhawar farashin kayayyaki fiye da kima, wannan lamari a kasar Sin yana kan wani matsakaicin mataki, inda babban bankin kasar ya yi imanin cewa, matakin zai daidaita.

A gaskiya dabarun kasar Sin suna haifar da da mai ido, domin suna tallafawa al’ummar kasar da yan kasuwar kasashen ketare har ma da taimakwa bunkasar tattalin arzikin kasashen dake hadin gwiwa da ita da ma duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)