logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda guda biyar

2022-07-19 09:56:57 CMG Hausa

Hukumomin tsaron Najeriya sun bayyana cewa, an yi nasarar kashe a kalla ’yan ta’adda guda 5, a wani samame na baya-bayan nan kan yaki da ta’addanci, da jami’an tsaron kasar suka kaddamar a yankin arewacin kasar.

Wata sanarwar da kakakin rundunar tsaron kasar Bernard Onyeuko ya fitar, ta bayyana cewa, an gano tarin makamai da alburusai da ’yan ta’addan ke amfani da su, a wani samame na daban da aka kai tsakanin ranakun 15 zuwa 17 ga watan Yuli, a jihohin Benue da Katsina dake arewacin kasar.

Onyeuko ya ce, an kashe ’yan ta’adda uku, sannan wasu da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga, bayan wani samame da sojojin suka kai a unguwar Sankera, dake karamar hukumar Ukum a jihar Benue dake yankin arewa ta tsakiyar Najeriya a ranar 15 ga watan Yuli.

A cewarsa, an kai harin ne bisa sahihan bayanan sirri da aka samu. Ya bayyana cewa, ’yan ta’addan sun gwabza kazamin fada da sojojin, amma karfin wuta na sojojin ya ci karfinsu, yana mai cewa, sojojin sun kuma kwato babura 18 da mayakan ke amfani da su.

Onyeuko ya ce, an kashe ’yan bindiga biyu a wani samame na daban, da sojojin suka kai kauyen Falalen-Jaja dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina dake yankin arewa maso yammacin kasar ranar Lahadin da ta gabata. (Ibrahim)