logo

HAUSA

Wani dan kasuwan kasar Sin ya bullo da shirin magance matsalar gurbataccen ruwa sha a nahiyar Afirka

2022-07-18 09:47:59 CMG Hausa

A yayin da yake kewaya birane da kauyukan Afirka, don tallata wayar salula kirar Tecno, Zhong Yanxiong mai shekaru 34 ya fahimci yadda kalubalen rashin ruwan sha mai tsafta ya yi kamari a nahiyar.

A yayin wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya a ofishin kamfaninsa dake birnin Nairobin kasar Kenya, Zhong ya bayyana cewa, zamansa na shekaru shida a Afirka, ya sa ya kara fahimtar matsalar ruwan sha mai tsafta da ake fuskanta a nahiyar, wanda hakan ya zaburar da shi shiga cikin wadanda za su warware wannan matsala.

Ya kara da cewa, na’urorin tace ruwa da ake kira RO purifiers da ake sayar da su a kasuwannin kasar Kenya, sun kai kudin kasar Kenya shillings 50,000, wato kimanin dalar Amurka 423, har zuwa shilling 80,000, kuma jama’a na sayen na’urar ce duk bayan watanni 6, su kuma bayar da su haya, duk da haka, bai rage yawan kudaden da magidanta talakawa ke kashewa, wajen tace gurbataccen ruwa ba.

Zhong ya bayyana cewa, a halin yanzu, kamfanin iClear ya zabi Kenya don gwada tsarin bayar da hayar na’urorin tsabtace ruwa, kafin ya yi shirin shiga wasu kasashen Afirka. Ya kara da cewa sama da iyalai 200 da suka gwada na'urar, sun yaba matuka.

Zhong ya ce, an kera na'urorin tsaftace ruwan ne a kasar Sin, kuma za su iya shafe tsawon shekaru biyar zuwa goma ba su samu wata matsala, muddin aka kiyaye su yadda ya kamata. Yana mai jaddada cewa, kamfanin iClear na da burin kulla alaka kai tsaye da abokan hulda da kuma ilimantar da su kan yadda ake amfani da na'urorin yadda ya kamata. (Ibrahim Yaya)