logo

HAUSA

Wannan Abu Ya Sa Afirka Ta Zama Abin Koyi

2022-07-18 15:55:40 CMG Hausa

Yau 18 ga watan Yuli rana ce da MDD ta kebe don tunawa da Nelson Mandela. Idan an ba ni damar takaita ruhin marigayi Mandela da kalma daya, zan zabi “Hakuri”. Saboda ya taba bayyana cewa, “Lalata abu na da sauki, amma wanda ya dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya shi ne jarumi.”

A sabili da ruhinsa na hakuri, bayan da Mandela ya kammala zamansa na shekaru 28 a gidan kurkuku, kuma ya zama shugaban kasa bakar fata na farko a tarihin kasar Afirka ta Kudu, bai nemi yin ramuwar gayya ga mutanen da suka taba cin zarafinsa ba. Don neman ganin an kafa wata sabuwar kasa, da samun sulhu tsakanin kabilu daban daban na kasar, ya nuna hakuri ga ‘yan kasarsa fararen fata, ta yadda a karshe dai ya cimma burin kare hakkin bakaken fata da kuma tabbatar da zaman daidaito a tsakaninsu da fararen fata.

A sauran kasashen Afirka ma, muna iya ganin yadda ra’ayi na hakuri ke taka muhimmiyar rawa. Misali a kasar Rwanda. Bayan abkuwar kisan kiyashi a shekarar 1994, wanda ya haddasa mutuwar mutane miliyan 1 a kasar, ba a ga wata ramuwar gayya daga ‘yan kabilar Tutsi ba. Maimakon haka, abun da aka yi shi ne neman samun maslaha. Cikin ‘yan kabilar Hutu dubu 120 da suka sa hannun kisan kiyashin, ban da yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 90 da suka fi taka rawar aikata laifukan, sauran sun samu damar gyara halinsu. Hakurin da aka nuna ya tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan al’umma, inda wannan yanayi ya sa kasar kiyaye saurin karuwar tattalin arzinta na kashi 70% ko fiye da haka, tun bayan shekarar 2003.

Abin takaici shi ne, ra’ayi na hakuri da marigayi Mandela da sauran ‘yan Afirka ke da shi, har yanzu bai yi tasiri a wasu wurare ba, musamman ma babbar kasar da take daukar kanta a matsayin mai kare dimokuradiya da hakkin dan Adam. A wannan kasa ra’ayin bambancin launin fata ya zama ruwa dare, inda yiwuwar ‘yan sanda su kama bakar fata ta ninka ta farar fata har sau 6. Kana an taba ganin yadda wani dan sanda ya danne wuyan wani saurayi bakar fata da gwiwa, har ya kashe shi, da yadda ‘yan sanda suka bindige wani bakar fata da ba shi da makami, wanda har aka samu raunukan bindigogi 60 a jikinsa, al’amuran da suka sanya al’ummar duniya cikin kaduwa.

Wannan kasa, ko da yake tana da karfi sosai a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, amma tana ci gaba da fama da yanayi na koma baya, ta fuskar zaman daidaito a tsakanin al’umma, da kare hakkin dan Adam. Yadda ake nuna rashin adalci a kasar, shi ma ya sa ta yi kokarin daukar matakai na son kai a duniya, ba tare da lura da bukatun sauran kasashe ba. Abubuwan da ya kamata wannan kasa ta koya daga kasashen Afirka, suna da yawa. (Bello Wang)