logo

HAUSA

AU ta yi kira da a gaggauta raya tsarin dunkulewar Afirka gu daya da masana’antun nahiyar

2022-07-18 10:19:11 CMG Hausa

An gudanar da taron koli na tsakiyar shekara na kungiyar AU karo na 4 a birnin Lusaka, babban birnin kasar Zambiya jiya Lahadi, inda shugabannin kasashen Afirka 13, suka yi kira ga membobin kungiyar AU da su sa kaimi ga raya yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka wato AfCFTA, da gaggauta aiwatar da dunkulewar Afirka gu daya da masana’antun nahiyar.

Shugaban karba-karba na kungiyar AU na wannan karo kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bayyana a gun taron manema labaru bayan taron tattaunawar cewa, taron ya tattauna muhimmancin dunkulewar kasashe Afirka, da inganta harkokin cinikayya cikin ‘yanci tsakanin yankunan. Shugabannin da suka halarci taron, sun amince cewa, za su aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA, a kokarin rage shingen ciniki tsakanin yankuna da kuma inganta hada-hadar kasuwanci.

Shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, har yanzu kasashen Afirka da dama, ba su cimma burin samar da abinci da kansu ba, wasu kuma suna fuskantar matsalar karancin abinci. Don haka, ya yi kira ga kasashen Afirka, da su kara zuba jari domin bunkasa ayyukan gona da daga darajar kayayyakin amfanin gona. (Zainab)