Sudan ta sake bude kan iyakarta da Habasha domin warware takaddamar dake tsakaninsu
2022-07-18 10:28:15 CMG Hausa
Kasar Sudan, ta yanke shawarar bude mashigar Galabat dake kan iyaka da kasar Habasha jiya Lahadi, a kokarin da take yi na karfafa amincewa da kuma warware takaddamar dake tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar da kwamitin tsaro na harkar soji na kasar Sudan ya fitar, ta bayyana cewa, a wani mataki na kokarin da shugabannin kasashen biyu ke yi, na magance matsalolin kan iyaka, kwamitin ya yanke shawarar bude mashigar Galabat daga jiyan.
A cewar sanarwar, majalisar ta kuma yanke shawarar kara sanya ido, kan iyakokin kasashen biyu, da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu, domin dakatar da zirga-zirgar masu dauke da makamai a kan iyakar.
Tun a watan Satumban shekarar 2020 ne, iyakar Sudan da Habasha ke fama da tashe-tashen hankula da kazamin fada tsakanin bangarorin biyu.
Kasar Sudan dai ta zargi sojojin Habasha, da goyon bayan kwace filayen ’yan Sudan da manoma suka yi a gundumar al-Fashaga da ke kan iyakar kasashen biyu. (Ibrahim)