logo

HAUSA

AU kaddamar da wani dandali na gargadin wuri domin magance rashin tsaro

2022-07-17 16:42:57 CMG Hausa

Tarayyar Afrika AU, ta kaddamar da wani dandali dake da nufin yin gargadin wuri domin kare aukuwar rikice-rikice da inganta zaman lafiya a nahiyar.

Mataimakiyar shugaban AU Monique Nsanzabaganwa, ta bayyana yayin kaddamar da dandalin a gefen taron majalisar zartarwar AU karo na 41 cewa, dandalin na musayar bayanai kan gargadin wuri da kare aukuwar rikici, zai taka muhimmiyar rawa wajen kare aukuwar rikice-rikice a nahiyar, haka kuma yana da alhakin ganowa da sauya barazana zuwa zaman lafiya.

Ta ce ana sa ran dandalin zai gina juriya da kwanciyar hankali a nahiyar da inganta musayar bayanai tsakanin kasashe mambobin tarayyar, tana mai cewa, ya kamata kasashen su kara mayar da hankali kan tsarukansu na gargadin wuri bisa la’akari da sarkakiyar da barazana ke da shi ga samar da zaman lafiya.

A nasa bangaren, kwamishinan AU mai kula da harkokin siyasa da tsaro da zaman lafiya, Bankole Adeoye, ya ce dandalin zai yi amfani da sabbin fasahohi wajen yin gargardin wuri ga kasashen AU kan barazanar tsaro.