logo

HAUSA

AU ta yi kira da a dauki nagartacciyar dabara domin cimma bukatun makamashi na nahiyar

2022-07-16 15:44:27 CMG Hausa

Tarayyar Afrika AU, ta ce nahiyar Afrika na bukatar nagartacciyar dabarar cimma bukatunta na makamashi.

Kwamshinar AU mai kula da makamashi da ababen more rayuwa, Amani Abou Zeid, ta ce yanayi mai sarkakiya da nahiyar ke ciki game da samun hidimomin makamshi mai tsafta, na alamta bukatar amfani da dukkan albarkatun makamashi da take da su, ciki har da wadanda ake iya sabuntawa da ma wadanda ba a iya sabuntawa.

Ta ce daga gajere zuwa matsakaicin zango, albarkatun man fetur, musammam danyen gas, za su taka muhimmiyar rawa wajen fadada samar da makamashi mai tsafta, baya ga gaggauta amfani da wadanda ake iya sabuntawa.

Jami’ar ta bayyana haka ne yayin wata hira da manema labarai a gefen taron tsakiyar shekara na tarayyar.

A cewarta, kalubalen da COVID-19 ta haifar da rikicin Rasha da Ukraine, na bukatar Afrika ta gaggauta duba yuwuwar samar da wani tsari na tabbatar da wadatar nata makamashi, wanda kuma zai inganta cinikayya tsakanin kasashen nahiyar da karfafa samar da karin man fetur da iskar gas.

Ta ce a shirye nahiyar take ta yi amfani da damarmakin dake akwai daga sauye-sauyen da ake gani a duniya, tare kuma da kokarin magance munanan tasirinsu. (Fa’iza Mustapha)