logo

HAUSA

Masaniyar Kenya: Tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya

2022-07-16 16:08:46 CMG Hausa

Masaniyar tattalin arziki dake aiki a jami’ar Riala Beatrice ta Kenya, Mathiri-Mysore, ta ce tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya, duk da cewa, kasar tana fama da cutar COVID-19 da sauye-sauyen yanayin siyasar duniya.

Mathiri Mysore, ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da manema labaran kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan.

Ta kara da cewa, kasar Sin ta gamu da matsala yayin da take fama da yaduwar cutar a wasu sassanta, amma sai ta fitar da manufofi a jere domin daidaita tattalin arzikin cikin nasara.

A ganinta, kudin shigar yawancin al’ummun kasar Sin yana da yawa, don haka kasar ke aiwatar da manufar habaka bukatun gida, a sa’i daya kuma, ta yi kokarin kafa sabon tsarin raya kasa domin tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki.

Mathiri-Mysore ta yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin tana mai da hankali kan kirkire-kirkire bisa dogaro da kanta, lamarin da ya kai ta ga samun babban ci gaba a fannin sabbin fasahohin zamani. Har ila yau, ta ce gwamnatin kasar Sin ta cimma burinta na tabbatar da lafiyar al’ummunta ta hanyar samar da isassun rigakafin cutar COVID-19 da masanan kimiyya na kasar suka nazarta. A cewarta, abun da ya fi burge al’ummomin kasa da kasa shi ne, yadda kasar Sin ta samar da tallafi ga kasashen da suke bukata a kan lokaci, musamman ma ga kasashen Afirka, wadanda suke fama da yaduwar annobar. (Jamila)