logo

HAUSA

Hauhawar farashi a Nijeriya ya kai kaso 18.6, adadi mafi koli cikin shekaru 5

2022-07-16 15:11:03 CMG Hausa

Alkaluman hukumar kididdiga ta Nijeriya, sun bayyana cewa, matakin hauhawar farashi a Nijeriya ya kai kaso 18.6 a watan Yuni , wanda ya karu daga kaso 17.71 da ya kasance a watan Mayu.

Adadin shi ne mafi yawa da aka samu a kasar mafi yawan al’umma a Afrika, tun bayan watan Junairun 2017 da ya kai kaso 18.72.

Alkaluman farashin kayayyakin masarufi, wanda shi ne ma’auni mafi girma na hauhawar farashin kayayyaki, ya karu da maki 0.85, idan aka kwatanta da kaso 17.75 da ya kasance a watan Yunin 2021.

A cewar hukumar ta NBS, an samu karuwar farashi a dukkanin rukunonin kayayyakin masarufi, inda hukumar ta ce hauhawar farashin kayayyaki na da alaka sosai da karuwar alkaluman farashin kayayyakin abinci, inda alkaluman bangaren ya kai kaso 20.60 a watan Yuni, adadin da ya karu daga kaso 19.5 na watan Mayu. Watanni 4 a jere kenan, alkaluman na karuwa. (Fa’iza Mustapha)